Home Kasashen Ketare Zaɓen Amirka: Biden ya lashe jihohin New York, Washington da wasu 9

Zaɓen Amirka: Biden ya lashe jihohin New York, Washington da wasu 9

180
0

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Amirka, inda shugaba mai ci Donald Trump na Republican ke fafatawa da Joe Biden na Democrats.

Ya zuwa lokacin haɗa labarin nan dai, kafafen yaɗa labarai na hasashen shugaba Trump ya yi nasara a jihohi 13 da suka haɗa da; Indiana, Kentucky, Oklahoma, Tennessee, da West Virginia – jihohin da dama ya samu nasara a zaɓen 2016.

Yayin da Biden shi kuma ya samu nasara a jihohi 11 da suka haɗa da jiharsa ta haihuwa Delaware, da babbar jiha New York da kuma babban birnin ƙasar watau Washington, kuma kamar dai Trump, suma waɗannan jihohi duka Hillary Clinton ta samu nasara a kansu a zaɓen 2016.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply