Home Kasashen Ketare Zaɓen Amirka: Daga ƙarshe dai China ta taya Biden murna

Zaɓen Amirka: Daga ƙarshe dai China ta taya Biden murna

119
0

A ƙarshe dai kasar China ta taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amirka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris murnar lashe zaɓen da suka yi.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Wang Wenbin ne ya bayyana haka a wani taro da ya yi da manema labarai.

Wang Wenbin ya ce “Muna mutunta zabin da jama’ar Amirka suka yi don haka Muna taya Mista Biden da kuma Misis Kamala Harris murnar nasarar da suka yi.”

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply