Home Kasashen Ketare Zaɓen Amirka: Iƙirarin maguɗin zaɓe gurgunta demokraɗiyya ne – Obama

Zaɓen Amirka: Iƙirarin maguɗin zaɓe gurgunta demokraɗiyya ne – Obama

158
0

Tsohon shugaban Amirka Barack Obama ya ce jigajigan jam’iyyar Republican na gurgunta demokraɗiyyar ƙasar ta hanyar goyon bayan zarge-zargen shugaba Trump na maguɗin zaɓe, waɗanda ba su da makama.

A wata fira da ya yi da CBS News, wadda za a saka a ranar Lahadi, Obama ya ce a bayyane take ƙarara cewa Joe Biden ne ya lashe zaɓen na bana.

Tuni dai shugaba Trump ya ƙaddamar da tawagar lauyoyin da za su ƙalubalanci zaɓen, saidai kuma har yanzu ba su bada wata hujja da za ta tabbatar da zargin nasu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply