Home Kasashen Ketare Zaɓen Amirka: Ana zargin Donald Trump da Joe Biden da lalata da...

Zaɓen Amirka: Ana zargin Donald Trump da Joe Biden da lalata da mata

87
0

Ɗan takarar shugabancin Amirka a ƙarƙashin jam’iyyar Democrat Joe Biden ya ƙaryata zargin keta haddin tsohuwar mai taimaka masa Tara Reade, shekaru 30 da suka wuce.

Biden ya buƙaci a nemo duk wasu bayanai a rumbun bayanan majalisar dattawan ƙasar don gano duk wani kundi da ke nuna Ms Reade ta gabatar da wani ƙorafi mai kama da wannan.

A watan da ya gabata ne dai ta kai koken an keta haddin ta ga ofishin ƴan sanda sai dai ba ta ambaci, sunan Biden ba.

Joe Biden dai na yin takara ne da Shugaba Donald Trump na Republican wanda ke fuskantar zarge-zargen keta haddi daga wasu mata 25.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply