Home Kasashen Ketare Zaɓen Nijar: Bazoum ya doshi zama shugaban kasa

Zaɓen Nijar: Bazoum ya doshi zama shugaban kasa

54
0

Dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki Malan Bazoum Mohamed na kan gaba a cikin sakamakon zaben da hukumar zaben CENI ke bayyanawa.

A jimilce dai dan takarar na PNDS na da kuri’u sama da miliyan biyu yayin da Mahaman Ousman na jam’iyyar RDR Tchanji mai hamayya keda kuri’u sama da miliyan daya da dubu dari hudu

Wannan sakamakon dai na kananan hukumomi 210 ne cikin 266 da ake da su a kasar kuma a wata ganawa da mataimakin shugaban hukumar zaben ya yi da wata kafar yada labarai ya ce sakamakon da ya rage ba zai iya sauya akalar sakamakon na yanzu ba musamman ta la’akari da kananan hukumomin da suka rage inda Bazoum ne ya samu nasara a zaben zagaye na farko.

Duba yadda jadawalin sakamakon zaɓen yake a hoto na ƙasa 👇

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply