Home Kasashen Ketare Zaɓen Nijar ya zama INCONCLUSIVE

Zaɓen Nijar ya zama INCONCLUSIVE

138
0

Jamhuriyar Nija za su sake zaben shugaban kasa a zagaye na biyua ranar 21 ga watan Fabrairu domin fitar da sabon shugaban kasar.

A sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar CENI ta fitar ranar Asabar da ta gabata, ya nuna cewa ba wani dan takara cikin masu neman kujerar, su 30 da yake da rinjaye a zaben da ya gudana a ranar 27 ga watan Disambar da ya gabata.

Domin zama zababbe ana bukatar dan takara ya samu kaso 50.1% na jimillar kuri’ar da aka jefa baki daya.

Zagayen farko dai na zaben an yi shi ne a ranar 27 ga watan Disambar 2020 inda ƴan takara 28 suka nemi kujerar ta shugaban kasa ciki harda Mohammed Bazoum dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya.

CENI ta shaida cewa Bazoum ya samu kaso 39.33% cikin 100 da kuri’a 1,879,000, yayinda Mohammed Ousmane na jam’iyyar RDR Canji ya samu kaso 16.99% da kuri’a 811,838.

Za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen ne tsakanin Tsohon ministan harkokin waje, Mohammed Bazoum na jam’iyya mai mulki da tsohon shugaban kasar Mahamane Ousmane a ranar 21 ga watan Fabrairu 2021.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply