Home Labarai Za a ƙaddamar da gasar ƙwallon hannu ta ƴan kasa da shekara...

Za a ƙaddamar da gasar ƙwallon hannu ta ƴan kasa da shekara 12 a Sokoto

148
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

A gobe lahadi ne za’a fara gasar wasannin kwallon hannu ta kasa a jihar Sakkwato

A yau assabar ne za’a soma tan-tance ‘yan wasan da suka iso jihar Sakkwato a jiya daga dukkanin sauran jihohin Najeriya inda ake sa ran bude wasannin kwallon hannu ta kasa ta ‘yan shekaru goma sha biyu zuwa sha biyar a jihar Sakkwato a gobe lahadi

A jiy Juma’a ne mahalarta wasannin daga jihohin Najeriya suka sauka jihar Sakkwato don bude gasar.

Zaratan ‘yan wasan kwallon hannun da suka fito daga sassan kasar zasu shafe kwanakki goma suna fafatawa.

Tuni dai gwamnatin jihar ta gina filayen wasanni maban-banta guda goma sha daya sakamakon karbar bakuncin wannan gasar wasan kwallon hannu da jihar zata yi, ciki ko har dana masu lalura ta musamman.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply