Home Labarai Za a ɗaga darajar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa Jami’a

Za a ɗaga darajar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa Jami’a

217
0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi alƙawarin ɗaga darajar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa Jami’a.

Tambuwal wanda ya faɗi haka a lokacin bikin cikar Kwalejin shekara 30 da kuma yayen ɗalibanta karo na 22, ya ce matakin ɗaga darajar kwalejin ya biyo bayan irin tarihin da ta kafa.

Gwamnan ya ce daga cikin matakan ɗaga darajar makarantar, tuni aka amince da gina ɗakunan ɗalibai, bene mai hawa biyu da zai ɗauki ɗalibai 400.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply