Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta binciki musabbabin yawan samun mace-macen mutane a fadin jihar.
Gwamna Aminu Masari ya ce gwamnatin ta horas da masu ilmin gano nau’in cutuka domin su gudanar da aikin binciken.
Gwamnan yace gwamnati ta samu rahoton yawaitar mace-macen mutane musamman masu manyan shekaru kafin su je asibiti a gano abin da ke damunsu.
Ya ce kwararrin za su dauki samfurin wadanda suka rasu, don su tabbatar da gano cutar corona ce ko a’a.
