Home Coronavirus Za a buɗe wuraren ibada da kamfanoni kaɗai bayan gama tantance su...

Za a buɗe wuraren ibada da kamfanoni kaɗai bayan gama tantance su – Gwamnan Lagos

216
0

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ce jami’an gwamnati za su ziyarci masallatai, coci-coci da kamfanoni don tantance irin shirin da suka yi na sake bude su.

A cewar sa, Bada tazara da tabbatar da tsabta na daga cikin abubuwa da za su tabbatar da sake bude wurare ibada.

Sanwo-Olu, ya bayyana haka a lokacin wani taron ‘yan jarida jiya Lahadi, bayan taron majalisar tsaron jihar a gidan gwamnatin jihar da ke Marina.

Ya yi bayanin cewa duba da girman tattalin arzikin jihar da yawan wuraren kasuwancin da ke jihar, babu yadda za a yi gwamnati ta ci gaba da rufe wuraren kasuwancin na din-din-din.

Gwamnan ya yi kira ‘yan kasuwa, wuraren addini da mazauna jihar su zaunan yadda suke, a daidai lokacin da jihar ke kokarin bullo da hanyoyin da za a sake bude hada-hada.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply