Gwamnatin Nijeriya ta sake dawo da mutane dubu 48 da ke amfana da tallafin gwamnati da aka dakatar a jihar Nasarawa a shekaru biyu da suka shuɗe.
Hajiya Sadiya Umar Farouk ita ce ministan jin ƙai da kare afkuwar bala’o’i ta bayyana haka a wani taro da ta halarta a garin Lafiya na jihar Nasarawa.
Hajiya Sadiya ta kuma bayar da umurnin da a gaggauta dawo da waɗannan mutane da aka dakatar, ta kuma ce a kara yi wa masu ƙaramin ƙarfi rajista domin suma su amfana da shirin bayar da tallafin.
