Home Labarai Za a ci tarar dubu 250 da daurin wata guda ga wanda...

Za a ci tarar dubu 250 da daurin wata guda ga wanda ya ci zarafin jami’in Amotekun

56
0

Gwamnatocin jihohin kudu maso yamma za su ci tarar Naira dubu 250 ko daurin wata daya ko kuma duka, ga duk wani wanda ya muzgunawa jami’in rundunar tsaron Amotekun.

Sannan kuma babu wanda ke da hurumin shigar da jami’an na Amotekun kara kotu a kan duk abunda suka aikata a kan aikin su, saidai idan wani abu ne can na rayuwar su.

Wannan dai na kunshe ne a cikin kudirin dokar kafa hukumar tsaro ta jihar Ekiti ta shekarar 2020 da aka aikewa majalisar dokokin jihar.

Suma sauran gwamnonin yankin su tura kwatankwacin wannan doka ga majalisun dokokin su domin amincewa.

Sashe na 36 na dokar kafa hukuar ta ce duk wani wanda ya yi kokarin katsalandan ko cin zarafin jami’in Amotekun da gangan, a lokacin da yake gudanar da aikin sa, za ci shi tarar Naira dubu 250 ko dauren wata daya ko kuma ma a hade masa duka.

Kudirin dokar ta kuma ce dole ne shugaban da zai jagoranci hukumar ya zama tsohon jami’in soji da ya kai mukamin Major ko kwatankwacin sa a wata hukumar tsaron kasar.

Kudirin dokar ya kuma tanadar da da kafa hukumar Amotekun wadda za ta rika yin zama akalla sau hudu a cikin shekara.

Hukumar gudanarwar za ta kunshi kwamishinan ‘yan sanda na jiha da sauran wakilan hukumomin tsaron jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply