Home Labarai Za a cigaba da buga Firimiyar Nijeriya

Za a cigaba da buga Firimiyar Nijeriya

67
0

Za a cigaba da buga gasar Firimiyar Nijeriya a ranar Lahadin nan bayan shafe tsawon lokaci da aka yi ba a buga wasan ba.

Kwamitin tsare-tsaren gasar ya fitar da jadawali, a inda za a kara a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, da Heartland FC, ya yin da Wikki Tourist za ta ziyarci Nasarawa United. Kungiyar Plateau United kuwa za ta gwabza da Kwara United a gidanta, sai Akwa United za ta kara da Dakkada FC.

Jigawa United kuwa za ta karbi bakuncin Sunshine Stars, Lobi Stars ta ziyarci Ifeanyi Ubah FC har gida domin buga wasan. Ita kuwa Rivers United za ta kara ne da Enugu Rangers, ya yin da Kano Pillars za ta yi tattaki har gidan Adamawa United.

Warri Wolves kuwa za ta fafata da MFM FC a filin wasa na Agege, Abia Warriors ta buga wasa tsakaninta da Eyimba.

A dai wannan kakar, kwamitin tsare-tsaren ya fitar da gwaggwabar kyauta ga wanda ya cinye gasar ta 2020/2021, inda zai yi awon-gaba da zunzurutun kudi har milyan N75, na biyu kuma zai kwashe milyan N50 shi kuwa na uku zai tashi da milyan N35, sauran kungiyoyin kuwa za su tashi da kyautuka daban-daban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply