Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a fara aiki da rage harajin shigo da motoci Nijeriya –...

Za a fara aiki da rage harajin shigo da motoci Nijeriya – Hameed Ali

42
0

Hukumar hana fasa ƙwabri ta Nijeriya Kwastan, ta ce mai yiwuwa ragin haraji kan shigo da motoci da taraktoci na kashi 10 daga kashi 35 zai fara aiki a makon gobe.

Da yake bayyana haka ga ƴanjarida a Abuja, shugaban hukumar Hameed Ali, ya ce daga yanzu zuwa ko wane lokaci suna tsammanin sanarwa a hukumance daga ma’aikatar kuɗi ta tarayya dangane da lamarin.

Hameed Ali, ya ce ragin kuɗin shigo da motocin wanda ke cikin dokar kuɗi ta shekarar 2020, wani yinƙuri ne da hukumar kwastan ta yi, domin sauƙaƙa kuɗin sufuri a Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply