Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a fara aikin Layin Dogon Kano-Maraɗi da zai cinye $1.959bn

Za a fara aikin Layin Dogon Kano-Maraɗi da zai cinye $1.959bn

92
0

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin Mota-Engil don gina hanyar jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi, da zai lakume dala Biliyan $1.959bn.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran ma’aikatar Sufuri Eric Ojiekwe ya fitar a ranar Litinin, ya ce manufar aikin ita ce zagaye kasar da hanyoyin jiragen kasar.

Ministan ya ce hanyar za ta ratsa jihohin Kano, Jigawa da Katsina sannan ta zarce zuwa Jamhuriyar Nijar, inda za ta tuke a Maradi.

Ya ce kuma hanyar za ta ratsa garuruwan Danbatta, Kazaure, Daura, Mashi, Katsina da Jibiya.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply