Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a fara amfani da tsarin Bola-Jari a Nijeriya

Za a fara amfani da tsarin Bola-Jari a Nijeriya

215
0

Majalisar zartaswa ta Nijeriya ta amince wa ma’aikatar kula da muhalli kan kudirin ta na bullo da sabon tsarin yadda za a rika sarrafa shara zuwa mayar da ita abubuwan amfani ga al’umma.

Ministan muhalli Dr Muhammad Mahmoud shi ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar.

Mahmoud ya kara da cewa tuni ma’aikatar kula da muhalli ta bude wata sabuwar masana’antar sarrafa shara da kuma bola ta yadda za a rika sarrafa su zuwa daben farfajiyar gini (interlock),domin bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma gyara muhalli.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply