Hukumar tattara harajin cikin gida ta jihar Kaduna, KADIRS, ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da kudirin ta na karbar harajin ₦1,000 a duk shekara ga mazauna jihar domin bunkasa haraji daga shekarar 2021.
Shugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar ne ya furta haka a wani taro da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Dakta Zaid ya ce daga shekarar 2021, duk wani baligi da ke zaune a jihar zai biya jihar harajin ₦1000, kamar yadda sashe na 9 (2) na cikin dokokin harajin jihar ya tanadar.
