Home Labarai Za a fara gwajin ƙwaya ga ƴan matan da za su yi...

Za a fara gwajin ƙwaya ga ƴan matan da za su yi aure – NDLEA

285
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta ce akwai yiwuwar a fara gwajin kwaya ga duk budurwar da za ta yi aure da ma matan aure.

Shugaban hukumar na jihar Borno Mustapha Abdalla ne ya yi wannan furucin a lokacin lalata wasu kwayoyi da hukumar ta amshe.

Ya ce yanzu sharrin kwayoyin ya fara wuce matasa, har ya fara isa ga ‘yan mata da matan aure.

Mustapha Abdalla ya ce an shirya lalata kwayoyin ne, don tabbatar da cewa duk wata kwaya da aka kama, an kona ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply