Gwamnatin jihar Kaduna za ta fitar da masu gyaran ababen hawa daga cikin garin Kaduna zuwa wasu sassa daban-daban da ta kebe masu.
Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta KASTLEA Manjo Garba Yahaya Rimi ne ya sanar da haka yayin da yake jawabi a wurin taron da aka yi don kiyaye dokokin hanya a Kaduna.
Ya ce gwamnati za ta samar da sabbin wuraren gyare-gyaren ne a kan titin Kaduna-Abuja da Kaduna-Kachiya da Kaduna-Birnin Gwari, sai kuma Kaduna-Zaria.
