Home Labarai Za a gina babbar cibiyar kimiyyar zamani a Abuja – Pantami

Za a gina babbar cibiyar kimiyyar zamani a Abuja – Pantami

27
0

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami yace, a zaman majalisar zartarwa na Larabar nan, gwamnatin Nijeriya, ta amince a gina “National ICT Park” a babban birnin tarayya na Abuja.

Dakta Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook, bayan kammala taron majalisar zartaswa na mako-mako.

Pantami ya kara da cewa sabon ginin cibiyar zai kasance babbar shelkwatar dukkanin cibiyoyin fasahar zamani da ke fadin kasar nan, za kuma ta zama wajen horar da ‘yan kasa da kuma samar musu da sana’o’i ta wannan hanyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply