Majalisar zartaswar Nijeriya ta amince da gina layin-dogo daga Kano-Jigawa-Katsina-Jibiya zuwa Maradi, Jamhuriyar Nijar.
Ministan sufuri Mr Rotimi Chibuike Amaechi ne ya sanar da hakan bayan kammala taron majalisar zartaswar a Abuja.
Ministan ya ce, ma’aikatar ta aike da bukatu 2 na son yin aikin layin-dogon, kuma duk an amince da su.
