Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da a kafa makarantun musaya (Unity School) a yankunan masarautun jihar guda biyar kuma za su fara aiki daga zangon karatu na shekarar 2021/2022.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan taron mako-mako da majalisar ke gudanarwa, wanda aka yi a gidan Afirka, da ke gidan gwamnatin Kano.
Ya ce za a fara buɗe makarantun da azuzuwan, JSS I, JSS II da kuma JSS III, kuma za a ɗauki ɗaliban ne bisa cancanta ta hanyar gudanar da jarabawar da ta dace.
