Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a hana shigo da madara da kifi a Nijeriya – Sabo...

Za a hana shigo da madara da kifi a Nijeriya – Sabo Nanono

253
1

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan gaba kadan za ta hana shigowa da kifi da madara a fadin kasa baki daya.

Ministan aikin gona Alhaji Sabo Nanono ne ya bayyana haka ya yin da ya ke kaddamar da cibiyar bunkasa harkokin noma a jami’ar tarayya da ke Dutsen jihar Jigawa.

Sabo Nanono ya ce kafin daukar matakin sai gwamnatin tarayya ta kara yin nazari sosai kan kayayyakin da za ta hana shigo da su, saboda Allah ya albarkaci kasar da albarkatun kasa da ma hanyoyin kasuwanci daban-daban, hakan ya sa babu wani abu da ba za a iya kirkirarsa ba a kasar nan.

Ya kara da cewa “tuni shirin gwamnatin Nijeriya ya yi nisa na samar da kamfanonin da za su rika samar da madara domin hana shigo da ita daga kasashen waje.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply