Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a horar da matasa dubu 100 sana’o’i a Adamawa

Za a horar da matasa dubu 100 sana’o’i a Adamawa

186
0

Ma’aikatar habaka harkokin kasuwanci ta jihar Adamawa ta fara gudanar da rijistar matasan jihar marasa aikin yi da yawansu ya kai dubu dari.

Kwamashinan ma’aikatar James Ilya ya tabbatar da haka, inda ya ce, ya zuwa yanzu ma’aikatar ta yi wa matasa akalla dubu takwas rijistar da za a horas da su sana’o’i daban-daban.

Ya kara da cewa ma’aikatar na shirin zakulo matasan da suka kammala karatun su na gaba da sakandare daga fadin sassan jihar domin ba su bashi mai saukin biya domin bunkasa tattalin arzikin jihar, ya kuma bayyana cewa matasan za su samu wannan horo ne daga kafafen sadarwa na zamani domin kauce wa bazuwar cutar corona.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply