Gwamnatin jihar Katsina ta fara wani yunkuri na kafa hukumar Hisbah a jihar.
Katsina Post ta ba da labarin cewa tuni sashen zartaswa ya mika wa majalisa don tattaunawa a kai.
A ranar Talatar nan, majalisar dokokin jihar ta kakkabe wannan kudiri ta gabatar da shi a zauren majalisa a lokacin zamanta.
Bayanai sun ce yanzu haka kudirin ya tsallake karatu na daya a gaban majalisar.
