Gwamnatin Kano ta ce iska da tsawa sun lalata makarantu 3,000 a jihar.
Shugaban hukumar ilimin baiɗaya na jihar SUBEB, Dr Ɗanlami Hayyo ya bayyana haka a lokacin da yake zanta wa da jaridar Solacebase a ranar Litinin.
Ɗanlami, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa don kiƴasta makarantun da ruwan sama ya lalata, ya ce tun bayan saukar ruwan a watan Yuni, makarantu da dama sun lalace sakamakon iska da saukar mamakon ruwan sama.
Ya ƙara da cewa aƙalla za a kashe Naira biliyan ₦30bn wajen gyaran makarantun waɗanda yawancinsu na Firamare ne da Sakandire a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
