Ministan bada tallafi da kyautata rayuwar jama’a Sadiya Umar Farouq ta ce daga yanzu za a rage wa’adin masu aikin N-power zuwa kasa da shekaru biyu.
Ta ce hakan yana daga cikin tsarin da ake na sabunta shirin don ya zama ya isa ga kowa.
Ministar ta fadi haka ne a lokacin da take jawabi a wajen taron ma’aikatun da ke karkashin ta a ranar Laraba.
Ta ce ma’aikatar ta, ta yi bitar shirin domin karfafa shi da kuma fadada shi.
Daga cikin abubuwa da za a bullo da su sun hada da rage wa’adin masu amfana da shirin, kaddamar da shirin tallafawa masu karamin karfi a cikin al’umma wata N-SIP da kuma bada fifiko wajen tallafawa mata.
