Home Labarai Za a samar da ma’adanar bayanan ƴan gudun Hijira a Nijeriya

Za a samar da ma’adanar bayanan ƴan gudun Hijira a Nijeriya

114
0

Gwamnatin Nijeriya ta amince da samar da rumbun adana bayanan ƴan gudun Hijira da ke faɗin ƙasar.

Shugaban kwamitin Majalisar wakilai kan ƴan gudun Hijira Muhammad Jega ya bayyana haka lokacin da hukumar kula da ƴan gudun Hijirar ke kare kasafin kuɗinta na baɗi, ranar Alhamis a Abuja.

Jega, ya ce shugaba Buhari ne ya faɗi haka a ranar 11 ga watan Oktoba, lokacin da yake bayyana sha’awar gwamnatin na samar da cikakkun bayanai kan ƴan gudun Hijirar da zai taimaka wajen kula da su.

Shima babban Kwamishinan hukumar ƴan gudun Hijirar Sanata Bashir Muhammad ya ce ƙarancin kuɗi na kawo tsaiko wajen aiwatar da ayyukan hukumar yadda ya kamata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply