Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za a yanke famfon da ke kai ruwa barikin soji a Neja

Za a yanke famfon da ke kai ruwa barikin soji a Neja

102
0

Gwamnatin jihar Neja ta yi barazanar dakatar da tura ruwan shan da ta ke yi ga barikin soja da ma sauran barikokin jami’an tsaro na Minna bisa dalilin cewa tana bin su basussuka na kudaden ruwa da suka kai kimanin Naira milyan 700.

Kwamishinan kula da albarkatun ruwa Yusuf Suleiman ne ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Minna.

Tun a farko dai mataimakin shugaban hukumar kula da samar da ruwan sha a jihar Malam Aliyu Danladi Umar ya labartawa kwamashinan cewa ana bin rundunonin tsaron jihar bashin kudaden da su ka kai kimanin Naira milyan 700.

Hakan ya sa hukumar samar da ruwan sha a jihar ta bayyana cewa za ta samar da mitocin ruwa na zamani domin kauce wa irin wadannan matsaloli na rashin biyan kudin ruwa da dai-daikun mutane da ma hukumomi ke yi a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply