Dan wasan bayan kulob din Liverpool Virgil van Dijk ya samu mugun rauni a guiwarsa da ya yi sanadiyyar yi masa tiyata.
Kulob din ya tabbatar da hakan, inda ya ce dan wasan bayan ya samu wannan rauni ne a wasan da suka tashi kunnen doki da Everton.
Ba a dade da fara wasan ba, aka sauya shi bayan da ya samu raunin.
