Home Labarai Za ku iya sanyawa wayoyin ku katin ₦1 – MTN

Za ku iya sanyawa wayoyin ku katin ₦1 – MTN

125
0


Kamfanin sadarwa na MTN Nijeriya, ya ɓullo da wani sabon tsari na sanya kuɗin waya, daga Naira ɗaya zuwa Naira miliyan uku (₦3m).

Da yake magana wajen ƙaddamar da shirin a Lagos, babban jami’in cinikayya na kamfanin Adekunle Adebiyi, ya bayyana tsarin da aka yiwa laƙabi da topit a wani ɓangare na sauƙaƙa rayuwar jama’ar da ke amfani da layin sadarwar.

Ya ce tsarin zai taimaka wajen magance matsalolin kankare kati, ɓatan kati, ɓata lokaci wajen danna lambobi da kuma gurɓata muhalli.

Kamfanin ya kuma ce tsarin na topit ya samar da sauƙakƙiyar hanya ta cinikayyar katin waya da datan shiga intanet.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply