Gwamnatin jihar Jigawa ta ce cikin kasafin kudin badi za ta gina sabbin hanyoyin guda 8 a fadin jihar.
Gwamna Badaru Abubakar na jihar ne ya bayyana haka yayin da ya ke mika dabtarin kasafin kudin shekarar badi ga majalisar dokokin jihar.
Ya ce sabbin hanyoyi da za su gina sun hada da kwanar kuka zuwa Tafa, Farun daba zuwa Mai Tsami- Ba’auzini- shataletalen Karkarna, sai kwalta daga Hadejia zuwa garun gabas da dai sauransu.
