Home Labarai Za mu mayar da hankali wajen ayyukan more rayuwa – Buhari

Za mu mayar da hankali wajen ayyukan more rayuwa – Buhari

109
0

Sugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen kashe kuɗaɗe a fannin ababen more rayuwa, ta yadda za a sa mu a kammala ayyukan da ƴan kwagilar cikin gida suka fara.

Shugaba Buhari ya sanar da haka yayin da yake ƙaddamar da sabon ginin shelkwatar hukumar sanya idanu da kuma bunƙasa samar da iskar gas a garin Yenagoa na jihar Bayelsa da aka gudanar a fadar gwamnatin ƙasar.

Shugaban ya ce ginin wannan sabuwar shelkwatar ya nuna jajircewar gwamnatinsa wajen samar da ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply