Home Labarai Za mu tabbatar da amincewa da dokar man fetur PIGB – Gbajabiamila

Za mu tabbatar da amincewa da dokar man fetur PIGB – Gbajabiamila

73
0

Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya bada tabbacin cewa majalisar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen amincewa da kudirin dokar man fetur kafin karshen watan Yuni.

A cewar sa, kudirin dokar shi ne gaba-gaba a majalisar, kuma ‘yan majalisar za su fara zama kan sa nan ba da jimawa ba.

Gbajabiamila, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilan kwamitin kwararru, kan shawarwarin tafiyar da albarkatun kasa, jiya a Abuja.

Ya ce bangaren mai da iskar gas shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arzikin kasar a halin yanzu, don haka dole ne a yi aiki tare don inganta shi.

Ya kuma shaidawa bakin, majalisar za ta yi amfani da karsashi, da kirshin kasar da ta yi amfani da shi wajen aiwatar da kudirin dokar yarjejeniyar rabon arzikin kasa na karkashin teku, wajen aiwatar da wannan kudiri na man fetur.

Shugaban tawagar, kuma tsohon karamin ministan man fetur Odein Ajumogobia, ya ce sun kawo ziyarar ne domin samun fahimtar juna da hadin kai daga kakakin majalisar wajen aiwatar da wasu kudirorin doka da za su inganta tattalin arzikin kasar, wanda kudirin dokar ta man fetur na daya daga ciki.

Ya kuma yi bayanin cewa, babban abun da kwamitin ya sa gaba shi ne tabbatar da aiwatar da tsarin kyautata albarkatun kasa na man fetur da iskar domin amfanin ‘yan kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply