Home Labarai Za mu tabbatar da ingancin zabe a Nijeriya – Malami

Za mu tabbatar da ingancin zabe a Nijeriya – Malami

179
0

Babban lauyan gwamnatin tarayyar Nijeriya Abubakar Malami ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dukufa wajen inganta harkokin zaben kasar.

Malmi wanda kuma shi ne ministan shari’a ya fadi haka ne a lokacin wani taro kan harkokin zabe da gidan talabijin na Channels ya shirya a ranar Talata.

Ya ce ba kamar gwamnatocin baya ba, wanan gwamnatin ta kyale hukumar zabe ta INEC ta ci gashin kanta, tare da girmama duk wani mataki da shari’a ta dauka.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta ce ta dukufa wajen yin gyaran fuska ga dokar zabenn kasar daga nan zuwa karshen shekara, kuma ministan ya bada tabbacen cewa, shugaba Buhari zai amince da gyaran matukar bai ci karo da kundin tsarin mulkin kasar ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply