Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Za mu tabbatar ka shiga Next Level – Tabbacin Buhari ga Adesina

Za mu tabbatar ka shiga Next Level – Tabbacin Buhari ga Adesina

100
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba Akinwumi Adesina tabbacin cewa Nijeriya za ta goyi bayan ganin an sake zaben sa a matsayin shugaban bankin ci gaban kasashen Afrika AfDB karo na biyu.

Buhari ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin Adesina a fadar sa da ke Abuja, a ranar Talata.

Ya yi alkawarin cewa Nijeriya za ta yi aiki da dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki nna AfDB domin tabbatar da cewa an zabi Adesina a karo na biyu domin dorawa a kan ci gaba da ya kawo a karon sa na farko.

Kungiyar hadin kan Afirika dai ta zabi Adesina a matsayin dan takarar ta ba hamayya, saidai wasu masu ruwa da tsakin na kokarin ganin an sake binciken sa kan zarge-zargen da ake masa, wanda suke ganin bai cancanci ya ci gaba da shugabancin ba.

Da yake magana, Adesina, ya ce zarge-zargen 16 da ake masa babu wata shaida a kan su kamar yadda ka’idojin bankin suka tanada.

Tsohon ministan noman na Nijeriya, ya ce kwamitin ladabtarwa na bankin ya riga da ya wanke shi, kuma kiran da Amirka ta yi na a sake gudanar da binciken ya sabawa dokokin bankin.

Haka ma, majalisar wakilai ta Nijeriya ta yi kira ga hukumar bankin na AfDB da ya dakatar da duk wani bincike kan Adesina, a kyale doka ta yi aikin ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply