Home Labarai “Za mu tura ku Dajin Sambisa”, Burutai ya shaida wa kuratan sojoji

“Za mu tura ku Dajin Sambisa”, Burutai ya shaida wa kuratan sojoji

166
0
Buratai

Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Tukur Yusuf Buratai yace za a tura daukacin sabbin sojojin da ke amsar horo zuwa Dajin Sambisa domin yakar ayyukan ta’addanci da kare martabar kasa.

Buratai wanda ya yi wannan furuci a lokacin shirin tantancewa na karshe na daukar sabbin kananan sojoji na rukuni na 80 na kananan sojoji a sansanin ba su horo da ke dajin Falgore jihar Kano, yace Nijeriya za ta rike kambinta na daukar jajirtattu kuma nagartattun sojojin da za su kare mata mutunci.

Babban hafsan sojin ya bukaci sabbin daukar, da kada su ba shari’a wahala muddin sun san ba za su iya zuwa Dajin Sambisa ba to su tarkata kayansu su bar gidan soja, yana mai cewa rundunar soji ba za ta sake saurar matasan da ba su shirya taimaka wa Nijeriya kawar da ta’addanci ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply