Home Labarai Za a yanke wa ƴanta’adda hukuncin kisa a Adamawa

Za a yanke wa ƴanta’adda hukuncin kisa a Adamawa

87
0

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya gargadi ƴanta’adda da su shiga taitayinsu ko kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin kisa.

Ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar bangirma ga Gwagwari Ganye Umaru Sanda a karamar hukumar Ganye.

Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta saurara ko tausayawa duk wanda aka kama da laifin sace mutane ko ta’addanci a cikin jihar ba.

Fintiri ya shaida kokarin gwamnatinsa wajen aiki da sauran jami’an tsaro sannan ya yi kira ga shugabannin al’umma da su hada kai domin shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply