DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasaZaben 2027: INEC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamna

Zaben 2027: INEC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamna

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cikakkun sunaye da bayanan ’yan takarar gwamna da mataimakansu a fadin jihohin kasar, matakin da ya kawo karshen fargabar wadanda za su wakilci manyan jam’iyyu a babban zaben 2027.

Hukumar ta manna wadannan bayanai ne a cikin fom din EC9 a dukkan ofisoshinta da ke jihohin kasar a ranar Asabar. Sanarwar ta bayyana shekaru, matakin ilimi, da sauran takardun shaidar ’yan takarar da suka fito daga jam’iyyun APC, ADC, NDC, PDP, APM da sauran su.

Wannan mataki ya bude sabon babi na shirye-shiryen zaben 2027, inda ake sa ran fara yakin neman zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a watan Satumban 2026 zuwa 4 ga Fabrairun 2027, kafin kada kuri’a a ranar 6 ga Fabrairun 2027 kamar yadda jadawalin hukumar ya tanada.

Ga yadda adadin da jerin ‘yan takarar suka kasance a wasu jihohin:

  • Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fafata da ‘yan takara da suka hada da Aminu Abdussalam Gwarzo na jam’iyyar NDC, Mohammed Raji na Labour Party, da Muhammad Dalhatu na PDP.

  • Kaduna: Gwamna Uba Sani na APC zai fuskanci wasu ‘yan takara 17.

  • Sokoto: Jam’iyyun siyasa 19 ne za su fafata a zaben gwamnan jihar.

  • Zamfara: Gwamna Dauda Lawal zai kara da ‘yan takara 15.

  • Bauchi: Mutum 19 ke neman kujerar Gwamna Bala Mohammed, ciki har da mace guda, Lami Babageidam ta jam’iyyar ZLP.

  • Jigawa da Kebbi: Jigawa na da ‘yan takara 14, yayin da Kebbi ke da ‘yan takara 14.

  • Legas: Mutum 17 za su fafata, ciki har da Mataimakin Gwamna mai ci, Obafemi Hamzat na APC da Gbadebo Rhodes-Vivour na ADC.

  • Kwara: Shugaban majalisar dokokin jihar, Yakubu Danladi-Salihu na APC, zai fafata da Bolakale Kawu na PDP da wasu ‘yan takara 10.

  • Benue: Gwamna Hyacinth Alia zai fuskanci ‘yan takara biyar, ciki har da tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Michael Aondoakaa (SAN) na jam’iyyar PDP.

A gefe guda kuma, Kwamishinan INEC na Kasa, Mohammed Haruna, ya bayyana cewa za a buga dukkan muhimman kayayyakin zaben 2027 a cikin gidan Nijeriya.

Haruna ya ce takardun kada kuri’a da na sakamako duk a cikin gida za a buga su bayan an binciki karfin kamfanonin buga takardu na cikin gida. Ya kara da cewa za a ajiye kayan ne a babban bankin Nijeriya (CBN) domin rarrabawa a gaban ‘yan jarida, jami’an jam’iyyu, da kungiyoyin sa-ido.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa matsalar da hukumar ke fuskanta a yanzu ita ce takaita wa’adin shirye-shirye zuwa watanni shida maimakon shekara guda sakamakon sauye-sauyen da aka yi wa dokar zabe.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata