Home Kasashen Ketare Zaben Amirka: Uwar gidan Barrack Obama ta ki amsa kiran yin takara

Zaben Amirka: Uwar gidan Barrack Obama ta ki amsa kiran yin takara

73
0

Daga Saleem Ashiru Mahuta

A yayin da ake ganin cewar uwar gidan tsohon shugaba Barrack Obama kadai ce zata iya kayar da shugaban Kasar Amirka Donald Trump, a Juma’ar nan Michelle Obama ta bayyana cewar bata da ra’ayin yin takarar shugabancin Kasar.

Michelle Obama matar tsohon shugaban Amirka

Obama ta bayyana cewar tana da abubuwan da zata iya yi don taimaka wa Amirkan ba sai lallai tayi takarar ba. To sai dai  wasu da dama na ganin cewar tana da cancantar da zata iya yiwaa Trump “kayen-raba-ni-da-yaro” a rumfunan zabe.

 

Wani Mazaunin kasar kuma mai yin wasan kwaikwayo Michael Moore ya shaida wa Jaridar The Hill cewar, mutanen kasar Amirka na matukar Kaunar Michelle, inda yake ganin cewar za ta iya karawa da Trump. Ya kuma bukace ta da ta amshi kiran yan kasar domin kawo masu ci gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply