Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kalubalanci shugaba Donald Trump kan cewa yana iza wutar da za ta iya kawo tashe-tashen hankula a kasar, wanda yin hakan bai dace ba.
An yi ta samun musayar kalamai tsakanin Joe Biden da Trump game da doka da oda a kasar ta Amurka.
Mr Biden ya ayyana cewa shugaba Trump na da rauni sosai, da ma sakaci a harkokin mulki, sannan yana tsoron tsawatarwa da magoya bayansa.
Ko a watan jiya, Shugaba Trump ya zargi abokin hamayyar ta sa da cewa yana da rauni, kuma bai dace a ce ya shugabanci Amurka ba.
