Home Kasashen Ketare Zaben Amurka: Trump ya ziyarci gangami a jihohin Maine da Minnesota

Zaben Amurka: Trump ya ziyarci gangami a jihohin Maine da Minnesota

96
0

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da kuma abokin takararsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden da ma sauran takwarorinsu na takarar shugabancin kasar daga jam’iyyu daban-daban sun kara wa magoya bayansu karfi tare da neman shawo kan wadanda ba su kai ga yanke hukuncin wanda za su zaba a babban zaben kasar da za a gudanar 3 ga watan gobe.

Shugaba mai ci Donald Trump ya halarci gangami a wasu daga cikin kananan jihohin arewa maso gabas na Maine da kuma Minnesota da kuri’unsu ka iya zama masu matukar mahimmanci.

Joe Biden da Trump din dai suna ci gaba da neman kuri’u 270 domin samun rinjaye cikin kuri’u 530 na electoral college.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply