Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a babban zaben da ya gabata, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce nasarar da gwamna Godwin Obaseki ya samu a zaben gwamnan jihar Edo da aka kammala a karshen makon nan, wata alama ce da ke nuni da cewa an kawo karshen siyasar ubangida a Nijeriya.
Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda kuma ya taya ilahirin al’ummar jihar Edo murna bisa jajircewarsu na zabar abin da ransu yake so.
