Babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Mohammed Adamu ya ba da umurnin da a takaita zirga-zirgar ababen hawa daga 11:59 na daren Juma’ar nan zuwa 6 na yamma a ranar Lahadi a shirye-shiryen zaben gwamnan Edo.
Babban sufeton ‘yansandan ya ce daukar matakin na a wani bangare na hana yaduwar makamai da muggan kwayoyi da kuma hana ayyukan ‘yan bangar siyasa.
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta kasa Frank Mba, ta roki mutane da su gudanar da zabensu cikin kwanciyar hankali da lumana.
