Wani gungun ‘yan siyasar adawa da ke takarar majalisar dokoki a jihar Diffa ya shigar da karar takardar zama cikakken dan kasa ta dan takarar jam’iyya mai mulki PNDS Tarayya Malam Bazoum Mohamed .
Wadannan ‘yan siyasa dai na bukatar a binciki takardar zama dan kasa ta Bazoum Mohamed ne domin tantance ta.
Daman dai tun da aka tsayar da Bazoum din a matsayin dan takara, jita-jita ke yawo a cikin kasar na cewa Bazoum din dan kasar Libya ne Sai dai magoya bayan shi na cewa wannan maganganun ‘yan adawa ne kawai.
A yanzu dai ranar 19 ga wannan watan na Nowamba za’a jira a gani da kotun tace za ta zauna a kan batun
