Home Kasashen Ketare Zaben Nijar: Moden FA Lumana ta mara baya ga RDR Tchanji

Zaben Nijar: Moden FA Lumana ta mara baya ga RDR Tchanji

103
0

Bayan dogon nazari da tattaunawa a tsakanin jagororin babbar jam’iyyar adawa Moden FA Lumana, jam’iyyar ta yanke shawarar mara wa dan takarar jam’iyyar RDR Tchanji tsohon shugaban kasa malan Mahaman Ousman baya.

A wata sanarwa, da jam’iyyar ta LUMANA ta fitar a yammacin Talatar nan ne aka sanar da wannan matsaya, sai dai Lumana ta ce ‘ya’yan jam’iyyarta su zabi Lumana a zaben ‘yan majalisar dokoki.

Babbar jam’iyyar adawar dai ta dauki wannan mataki biyo bayan fatali da takardun dan takararta Hama Amadou da kotun kundin tsarin mulki ta yi sakamakon taba yanke mishi hukuncin zaman gidan yari na shekara guda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply