Farfesa Pat Utomi, masanin harkokin tattalin siyasa a Nijeriya, ya ce sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga watan Agusta ya nuna cewa kuri’ar jama’a na iya yin galaba kan yunkurin yin magudin zabe a kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Utomi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar, inda ya yabawa al’ummar Osun bisa yadda suka fito suka kada kuri’a.
Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta bayyana gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 511,067 a kananan hukumomi 19 na jihar.
Babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, ne ya samu kuri’u 444,815 a kananan hukumomi 11 na jihar.
Da yake martani kan sakamakon zaben, Utomi ya ce al’ummar Osun sun nuna cewa idan ’yan kasa suka jajirce wajen kare kuri’arsu, za su iya dakile duk wani yunkuri na karkatar da sakamakon zabe.
Utomi ya kuma kwatanta sakamakon zaben Osun da abin da ya faru a Kano a shekarun baya, yana mai cewa jama’a na iya tabbatar da zabin da suka yi idan suka tsaya tsayin daka.
A cewarsa, yawan fitowar masu kada kuri’a da kuma jajircewarsu wajen kare zabin da suka yi na daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen karfafa dimokuradiyya a Nijeriya.
Ya kara da cewa darasin zaben Osun ya kamata ya zama abin karfafa gwiwa ga masu kada kuri’a yayin da kasar ke tunkarar babban zaben 2027.
Zaben Osun ya nuna masu kada kuri’a za su iya kawar da magudin zabe a Nijeriya – Pat Utomi
Farfesa Pat Utomi, masanin harkokin siyasa a Nijeriya ya ce sakamakon zaben gwamnan jihar Osun ya nuna cewa kuri’ar jama’a na iya yin galaba kan yunkurin yin magudin zabe a kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Utomi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya yaba wa al’ummar Osun bisa yadda suka fito suka kada kuri’a.
Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta bayyana gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 511,067 a kananan hukumomi 19 na jihar.
Babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ya samu kuri’u 444,815 a kananan hukumomi 11 na jihar.
Da yake martani kan sakamakon zaben, Utomi ya ce al’ummar Osun sun nuna cewa idan ’yan kasa suka jajirce wajen kare kuri’arsu, za su iya dakile duk wani yunkuri na karkatar da sakamakon zabe.
Utomi ya kuma kwatanta sakamakon zaben Osun da abin da ya faru a Kano a shekarun baya, yana mai cewa jama’a na iya tabbatar da zabin da suka yi idan suka tsaya tsayin daka.
A cewarsa, yawan fitowar masu kada kuri’a da kuma jajircewarsu wajen kare zabin da suka yi na daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen karfafa dimokuradiyya a Nijeriya.
Ya kara da cewa darasin zaben Osun ya kamata ya zama abin karfafa gwiwa ga ‘yan Nijeriya yayin da kasar ke tunkarar babban zaben 2027.
