Home Kasashen Ketare Zaben shugaban kasa a Nijar na musamman a cikin shekaru 60

Zaben shugaban kasa a Nijar na musamman a cikin shekaru 60

170
0

Jamhuriyar Nijar na fatan kafa gagarumin tarihi a karon farko a ranar Lahadi mai zuwa 27.12.2020.  Zaben shugaban kasa da za a yi a ranar zai kasance na farko da gwamnatin farar hula za ta mika wa wata zababbiyar gwamnati.

Bazoum Mohammed dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya

A cikin shekaru 60 da Nijar ta samu ‘yancin kai daga Turawan Faransa sojoji sun ta yin juyin mulkin da ya hana zababbiyar gwamnati mikawa ga wata gwamnatin dimukuradiyya. Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou na shan jinjina kan amincewa ya mika mulki ga wata sabuwar gwamnatin da yan Nijar za su zaba ba tare da yin dabara irinta shugabannin kasashen Ivory Coast da Guinea ba.

Albade Abuba 'dan takarar shugabancin Nijar a karkashin jami'iyyar MPR Jamhuriyya.
Albade Abuba ‘dan takarar shugabancin Nijar a karkashin jami’iyyar MPR Jamhuriyya.

Faransa ta yaba wa Issoufou kan wannan kokari sai dai ta ce gudanar da zaben cikin adalci da lumana zai zama babban abin koyi ga kasashen yammacin Afirka. Sai dai kuma Farfesa Bounty Diallo na jami’ar Yamai ya ce Shugaba Issoufou ba zai nemi wa’adi na uku ba saboda ba shi da wani zabin da ya wuce sallama daga madafun iko.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply