Home Kasashen Ketare Zaben Shugaban Kasa A Tunisiya Ya Gudana Karkashin Kulawar Jami’an Tsaro

Zaben Shugaban Kasa A Tunisiya Ya Gudana Karkashin Kulawar Jami’an Tsaro

72
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

‘Yan kasar Tunisia milyan 7 ne suka fita don kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa a ranar Lahadi.

Wannan zaben shi ne na biyu tun shekarar 2011 bayan juyin-juya-halin da aka fuskanta a kasar.

‘Yan takara 26 ne suke neman shugabancin kasar ta Tunisia a zagaye na farko.

Cikinsu kuwa ha da mai kafar watsa labarai Nabil Karoui da ya ke tsare a gidan yari bisa wasu zarge-zargen da ya musanta.

An dai jibge jami’an ‘yan sanda dubu 70,000 da karin sojoji dubu 30,000 a fadin kasar don saka idanu kan lamurran zaben.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply