Home Labarai Ta ba dan kishiyarta guba ya ci ya mutu

Ta ba dan kishiyarta guba ya ci ya mutu

295
0

Wata yar kimanin shekaru 20, mai suna Murja Ibrahim, ta shiga hannun hukuma bisa zargin kisan dan kishiyarta ta hanyar bashi guba.

GamboIsah wanda shi ne kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.

A cewarsa lamarin ya faru ne a kauyen Jidadi da ke ƙaramar hukumar Dandume na jihar bayan karar da mahaifin yaron da aka kashe ya gabatar.

Ana dai ci gaba da binciken Murja kafin a gurfanar da ita gaban kuliya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply